Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Ofishin Jakadancin Koriya Ta Arewa Ya Baude Zuwa Koriya Ta Kudu


Babban jami'i na biyu a Ofishin Jakadancin Koriya Ta Arewa a London, ya baude zuwa Koriya Ta Kudu, a cewar Ma'aikatar Hadin Kai Ta Koriya Ta Kudun

Thae Yong Ho ya isa Seoul, babban birnin Koriya Ta Kudu da shi da iyalinsa a cewar mai magana da yawun Ma'aikatar Jeong Joon-hee. "A halin yanzu gwamnati na kare su," in ji Jeong a wani taron manema labarai.

Jeong ya ce Thae ya gaya ma jami'an Koriya Ta Kudun cewa ya gudu ne saboda kyamar gwamnatin shugaba Koriya Ta Arewa Kim Jong Un, da sha'awar tsarin dimokaradiyyar Koriya Ta Kudu da kuma damuwa game da makomar 'ya'yansa.

An yi imanin cewa Thae ya yi aikin tsawon shekaru 10 a Ofishin Jakadancin Koriya Ta Arewa da ke London, inda aikinsa ne inganta mutuncin Koriya Ta Arewar, wadda ta sha caccaka saboda shirinta na nukiliya da kuma batun 'yancin dan adam. An yi imanin cewa Thae ne jami'in diflomasiyyar Koriya ta Arewa mafi girma da ya taba canza zuwa Koriya Ta Kudu.

A birnin Washington, Ma'aikatar Harkokin Waje ta ki ta yi takamammiyar magana game da wannan batu, sai dai kira da ta yi a kare 'yan gudun hijirar Koriya Ta Arewa da kuma masu nemar mafaka.

Jami'in gwamnatin Koriya Ta Arewa mafi girma da ya taba canza sheka zuwa Koriya Ta Kudu, shi ne Hwang Jang-yop, wani babban jami'in Jam'iyyar Ma'aikata mai mulki, wanda ya nemi mafaka a Koriya Ta Kudun a 1997.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG