Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Halaka Mutane Hudu a Amurka


Wasu mazauna yankin Texas suna ficewa daga gidajensu

Ruwan sama da aka aka yi ta tafkawa kamar da bakin kwarya, wanda da ya haifar da ambaliyar ruwa a ‘yan kwanakin nan a jihar Texas da ke kudancin Amurka, ya halaka mutane hudu, a cewar jami’an ba da agajin gaggawa.

Mazauna yankin da lamarin ya shafa suna duba yuwuwar ficewa daga gidajensu baki daya, yayin da ruwan ke kara haurawa.

Tuni hukumomin wasu yankunan suka tilastawa mazauna wasu unguwanni ficewa daga gidajensu.

Ambaliyar ruwan ta sa hanyoyi sun rufe kana an kulle makarantu, yayin da wasu masu ababan hawa suka makale akan hanya.

Ana tunanin ruwan saman zai karu, yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bukuwan ranar tunawa da dakarun Amurka da suka mutu suna bautawa kasar.

XS
SM
MD
LG