Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aman Toka Ya Halaka Mutane Shida a Indonesia


Yankin Gamber na kasar Indonesia da toka ta kwararo daga cikin dutse

Jami’ai a Indonesisa sun ce akalla mutane shida ne suka mutu, bayan aman toka mai tiriri da wani dutse ya yi.

Lamarin ya auku ne a jiya Asabar a dutsen da ake kira Sinabung da ke arewacin Lardin Sumatra, inda ya rika fetso toka akan kauyen Gamber, yankin da ake mai kallon mai cike da hadari, wanda kuma ke da tazarar tafiyar kilomita hudu daga dutsen.

Jami’ai sun ce har ya zuwa yau Lahadi, dutsen na cigaba da fitar da toka mai tiriri, lamarin da ya kara janyo cikas wajen baiwa masu ayyukan ceto damar gudanar da ayyukansu na neman wadanda suka tsira daga hadarin.

Rahotanni sun nuna cewa, dutsen ya kwashe shekaru aru-aru ba ya fitar da tokar sai a wannan karni na 21.

Shi dai wannan dutse na Sinabung, ya kasance daya daga cikin duwatsu 120 da kan yi amai a kasar ta Indonesia, wanda kan haddasa asarar rayuka saboda kusancinsa da yankin duwatsu ko tuddai da kan fetso wuta ko toka mai tiriri.

XS
SM
MD
LG