Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aminu Muhammad: Kungiyar Daliban Najeriya Za Ta Fara Zanga-Zanga Ranar Litinin


Aminu Adamu Muhammad.
Aminu Adamu Muhammad.

Muhammad, wanda dalibi ne da ke karatu a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, na fuskantar tuhuma kan zargin batawa uwargidan Najeriya Aisha Buhari suna inda yanzu haka yake tsare a gidan yari.

Kungiyar Daliban Najeriya ta NANS, ta ce za ta fara zanga-zanga ranar Litinin 5 ga watan Disambar idan har hukumomi ba su saki Aminu Muhammad ba.

Muhammad, wanda dalibi ne da ke karatu a jami’ar tarayya da ke Dutse a jihar Jigawa, na fuskantar tuhuma kan batawa uwargidan Najeriya Aisha Buhari suna.

A ranar Talata hukumomi suka gurfanar da shi a gaban wata kotu da ke Abuja kan wannan tuhuma.

Dalibin, wanda ke shekarar karatunsa ta karshe, ya ki amsa laifin da ake tuhumar shi akai. Kotun ta kuma tura shi gidan yarin Suleja kafin a ci gaba da karar.

Sai dai cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis, kungiyar daliban ta NANS, ta ce abin ya kai makura.

“Ya ku dalibai! duba da cewa mun bi dukkan zabin da muke da shi domin kaucewa yin fito-na-fito a kokarinmu na ganin an saki daya daga cikin mambobinmu, wanda aka kama, aka azabtar, aka ci mutuncisa, sannan jami’an gwamnati suka tsare shi, muna masu sanar da ku cewa, shugabancin wannan kungiya, ya yanke shawarar fara zanga-zanga.” Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Comrade Usman Umar Barambu ta ce cikin yanayi na yakewu.

Sanarwar ta kara da cewa, “kusan da cewa, za mu ci gaba da yin wannan zanga-zanga har sai an sake shi ba tare da an gindaya wani sharadi ba. Kuma kusan da cewa abin da ya shafi dayanmu, mu ma ya shafe mu.

“Wannan zanga-zanga ce da ke adawa da Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba da uwargidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari.” Shugaban kungiyar ta NANS, Barambu ya kara da cewa cikin sanarwar.

Ana dai tuhumar Muhammad ne bisa wani sakon Twitter da ya wallafa a watannin baya, wanda ya ce, “mama kin ci kudin talakawa an koshi,” lamarin da ya kai ga jami’an tsaro suka bi shi har farfajiyar jami’ar tarayyar da ke Duste suka kama shi tare da tusa keyarsa zuwa birnin Abuja kamar yadda rahotanni suka nuna.

Wata zanga-zanga da daliban jami'o'in Najeriya suka yi a shekarar 2018 (Twitter/@NANSNIG)
Wata zanga-zanga da daliban jami'o'in Najeriya suka yi a shekarar 2018 (Twitter/@NANSNIG)

Kafofin yada labarai da dama sun ruwaito cewa har gaban uwargidan shugaban kasa aka kai shi.

Sannan an yi zargin cewa, jami’an tsaro sun bugi Muhammad gabanin a gurfanar da shi a gaban kotu, lamarin da ya janyo kakkausar suka har daga kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty.

Tun da wannan al’mari ya faru, jami’an tsaro, Aisha Buhari da ita kanta fadar shugaban kasar ba su ce uffan ba, kuma dukkan yunkurin jin ta bakin uwargidan shugaban kasar da jami’an tsaro ya ci tura.

Sai dai duk da suka da suke sha, wasu da dama na ganin matakin da jami'an tsaron suka dauka akan dalibin ya yi daidai, duba da yadda ake zargin wasu na yin amfani da kafafen sada zumunta wajen yin batanci ga mutane.

XS
SM
MD
LG