Accessibility links

Amnesty Ta Zargi Kamfanin Shell kan Gurbata Yanayi a Kudancin Najeriya


Hoton mai kwance kan ruwa a yankin Ogoni na NIger delta a kudancin Najeriya, kusa da wata matatar mai ta 'yan fasa kwabri, 24 Maris 2011

'Yan yankin Niger-Delta sun bayyana gamsuwarsu da rahoton Amnesty dake nuna cewa kamfanin Shell yana dora laifin tsiyayar mai a kan matasa masu fasa bututu don satar mai domin ya kaucewa fuskantar shari'a

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi zargin cewa kamfanin mai na Shell, yana yin rufa-rufa sosai kan yadda ayyukansa yake gurbata yanayi a yankin Niger-Delta na kudancin Najeriya.

A cikin wani rahoton da ta bayar, kungiyar Amnesty ta ce kamfanin Shell yana yawan dora laifin gurbacewar yanayi a sanadin tsiyayar mai a kan 'yan yankin na Niger Delta dake fasa bututu domin satar mai.

Amnesty ta ce kokarin kaucewa fuskantar shari'a ne ya sa kamfanin na Shell yake yawan dora laifin tsiyayar mai a kan matasan yankin Niger Delta.

Wakilin Sashen Hausa, Lamido Abubakar, ya zagaya a cikin yankin domin jin ra'ayoyin jama'a game da wannan rahoto na kungiyar Amnesty, ya kuma aiko mana da wannan rahoto...

XS
SM
MD
LG