Accessibility links

A karo na biyu kennan cikin wannan shekara, kamfanin haka da sarrafa danen mai, Royal Dutch Shell ya rufe daya daga cikin manyan bututunsa a kudancin Najeriya, domin yi masa gyara bayan da barayin mai suka lalata shi.

WASHINGTON, D.C - Kamfanin Shell yace ya rufe bututun Nembe Creek ranar Litinin domin toshe famfunan mai da barayi suka kafa, da kuma binicika laifuka makamantan haka.

Rufe bututun zai rage adadin mai da kamfanin yake sarrafawa na barrel 150,000 a rana.

Saboda haka, Shell din ya bayanawa kamfanin hada-hadar mai na Bonny Crude Light Export cewa ba zai iya samar da man da yayi alkawari ba.

Direktan Shell a Najeriya, Muti'u Sunmonu yace tun da aka kafa bututun wanda yace tazarar kilimita 97 a shekara ta 2010, barayin mai sun ffar masa, suna fasawa domin satar mai.

Sunmonu ya fada a wata sanarwa cewa satar danyen mai na cigaba da shafar mutane, da muhalli da tattalin arzikin Najeriya, kuma yayi kira da gwamnati ta dauki mataki cikin hanzari domin warware wannan matsala.
XS
SM
MD
LG