Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Birtaniya Sun Ce Akwai Yiwuwar Sake Kai Hare Hare A Abuja


Wasu motoci da mahara suka kona
Wasu motoci da mahara suka kona

Amurka da Burtaniyan sun fidda takardun gargadi ga yan kasashen nasu biyo bayan mummunan harin ta'addanci da aka kai gidan gyaran hali na koje dake yankin babban birnin Tarayyar Najeriya

Amurka ta shaidawa Amurkawan dake Abuja cewa akwai yiwuwar kara samun matsalolin tsaro a ciki da wajen yankin babban birnin tarayyar kasar,saboda haka dole su yi kaffa kaffa da takatsantsan har nan da makonni biyu masu zuwa.

Bugu da kari Amurka ta bukaci 'yan kasar nata da su guji bin kan hanyar filin jirgin sama na Abuja, inda ta nanne garin kuje yake ganin sha'anin tsaro na kara sukurkucewa a Najeriya, yana da kyau a guji yankunan da ake tababar amincinsu.

Kazalika ita ma Burtaniya taja hankalin 'yan kasarta da su yi taka tsantsan ganin yadda matsalar tsaron ke shiga wani sabon babi, inda tace su kuma guji yin bulaguro zuwa wasu jihohin kasar goma sha tara da ma na yankin Naija Delta.

XS
SM
MD
LG