Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da Qatar Sun Kulla Yarjejeniyar Dakile Daukar Nauyin Ta'addanci


Sakataren ma'aikatar harkokin tsaron Amurka Rex Tillerson da ministan harkokin kasashen ketare na Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani suna sa hannu a yarjejeniya MOU a Doha, Qatar, July 11, 2017.
Sakataren ma'aikatar harkokin tsaron Amurka Rex Tillerson da ministan harkokin kasashen ketare na Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani suna sa hannu a yarjejeniya MOU a Doha, Qatar, July 11, 2017.

A yunkurin da yake yi na warware rikicin dake tsakanin Qatar da kasashe hudu makwabtanta a yankin Gulf, Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson,yana Sa'udiyya a yau laraba, inda zai gana da jami’an kasashen dake zargin Qatar da goyon bayan ta’addanci.

Za a yi wannan tattaunawa a birnin Jeddah,kwana daya a bayanda Tillerson ya sanar da cewar Amurka da Qatar sun sa hannu a yarjejeniyar da ta bukaci Doha ta dauki matakan shawo kan daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Maganar Tillerson a Qatar "30
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:13 0:00

Ina nan a Qatar yau da irin himmar da shugaba Trump ya tafi Riyadh da ita a watan Mayu. Burin Amurka daya ne, a kawar da ayyukan ta’addanci daga doron kasa."

Sai dai kasashen Saudiya da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain da kuma Misira sun fada a wata sanarwa cewa, yayinda suke yaba yunkurin Amurka na yaki da ta’addanci, yarjejeniyar da aka sawa hannu jiya Talata bata isa ba, kuma zasu ci gaba da sawa Qatar ido sosai wajen dakile daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

Kasashen dai sun yanke huldar diplomasiya ne ranar biyar ga watan Yuni, suka dauki matakin rufe hanyoyin sufurin kasa da na sama da kuma na ruwa da Qatar. Kasashen da Saudiya ke jagoranta suna zargin Qatar da goyon bayan ayyukan ta’addanci, suka kuma ba Doha jerin sharuda goma sha uku da suke nema ta cika. Kasar Qatar tace a shirye take ta tattauna da nufin samun masalaha amma ba zata sadaukar da diyaucinta ba

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG