Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ce ta jaddada haka a jiya Laraba na tsagaita wutar a Aleppo da kewaye, wanda yarjejeniyar ta fara aiki a jim kadan bayan tsakar daren agogon kasar.
Gwamnatin Syria ta ce zata mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar a Aleppo, amma sun ce yarjejeniyar ta tsawon sa’o’i 48 ce kadai. A wata sanarwar ‘yan adawar Syria sun ce ya kamata ace an tsagaita wutar gaba daya ne ba a wasu zababbun wurare ba.
Kamar yadda Kakakin ‘yan adawa Salem al-Meslet yace, in ba haka ba to kuwa ba inda wannan yarjejeniyar zata je. Jami’ai a nan Amurka sun ce, duk da yarjejeniyar akwai rahotannin da ke cewa ana fada a wasu wuraren.
To amma duk da haka, idan aka dubi rikicin gaba daya, an samu yar dan lafawa. Amurka da Rasha ke kokarin shiga tsakanin tsagaita wutar don a samu daidaito tun a watan Fabrairun shekarar nan.