Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka, Korea Ta Kudu Na Shirin Fara Atisayen Soji


South Korean (blue headbands) and U.S. Marines take positions as amphibious assault vehicles of the South Korean Marine Corps fire smoke bombs during a U.S.-South Korea joint landing operation drill in Pohang, South Korea, March 12, 2016.

Amurka da Korea ta Kudu za su fara atisayen soji na hadin gwiwa na shekara-shekara da suka saba yi a ranar Talata mai zuwa.

Kafafen yada labaran kasar ta Korea ta Kudu sun ce an dan samu jinkirin kwana biyu da farawa, bayan da aka samu wani sojan kasar da cutar coronavirus.

A ranar Lahadi gamayyar hafsoshin sojin kasar suka ce cutar ta COVID-19 ce ta sa aka jinkirta atisayen.

A baya an tsara za a fara shi ne a yau Lahadi, amma kuma aka dage zuwa Talata bayan da gwaji ya nuna wani sojan kasar ta Korea ta Kudu ya kamu da cutar a ranar Juma’a, wanda asali aka tsara zai shiga atisayen, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya ruwaito.

Korea ta Arewa dai ta kan sa ido kan wannan atisayen hadin gwiwa na shekara-shekara, wanda take kallon sa a matsayin “atisayen shirin kaddamar da yaki.”

A ‘yan shekarun bayan nan, an rage gudanar da shi, a wani mataki na kokarin ganin an cimma matsaya a tattaunawar da ake yi na a kwance shirin da hukumomin Pyongyang ke yi na kara makamin nukiliya.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG