Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Harbe-harbe a Wajen Fadar White House


An yi harbe harbe a wajen fadar White House

Wani jami’in 'yan sandan ciki masu kare shugaban kasa ya fitar da shugaban Amurka Donald Trump ba shiri daga zauren ganawa da manema labarai na fadar White House daidai lokacin da ya ke yi masu bayani a kan coronavirus jiya Litinin a fadar White House, saboda harbe harbe a wajen ginin.

Trump ya dawo bayan mintoci kalilan ya kuma ce lallai an yi harbi har ma an kai wani asibiti. Ya ce wani jami’in tsaron kasa ne ya yi harbin kuma yana sa ran wanda aka harbe yana rike da makami ne.

Wakilin Muryar Amurka a fadar White House Steve Herman, da ya halarci taron, ya ce manema labarai sun ci gaba da kasancewa a dakin taron, yayin da aka dakatar da ayyukan White House.

Ma’aikatar tattara bayanan sirri ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG