Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Goyon Bayan Okonjo-Iweala Kan Shugabancin WTO


TSOHON HOTO: Okonjo-Iweala
TSOHON HOTO: Okonjo-Iweala

Tsohuwar Ministan kudin Najeriya, Ngozi Okonjo-Iweal, na shirin zama mace ta farko kuma ‘yan nahiyar afrika ta farko, da za ta shugabancin kungiyar hadahadar kasuwancin duniya WTO.

Hakan na zuwa ne bayan da abokiyar hamayyar ta Korea ta Kudu ta janye takararta a jiya Juma’a, bayan kuma da Amurka ta sauya adawar da take nunawa ga takarar ta ta.

Gwamnatin shugaba Joe Biden ta nuna kcikakken goyon bayanta ga Okonjo-Iweala a wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a, sanarwa da ta ambato irin kwarewar da take da ita musamman kan irin aikin da ta yi a Bankin Duniya baya ga jagorantar ma’aikatar kudin Najeriya.

Amurkan dai ta sha alwashin za ta yi aiki tare da ita kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

Wadannan al’amura biyu da suka faru, sun kawo karshen zaman rashin tabbas da ake yi kan shugabancin kungiyar kasuwancin ta duniya, sannan sun yi sharar fage ga mambobinta wajen kammala tabbatarwa da Okonjo-Iweala da mukaminta a matsayin shugaban kungiyar.

Gwmanatin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, ta ki amincewa da Okonjo—Iweala, duk da cewa, kwamitin da aka nada don zaben sabon shugaban kungiyar ya zabe ta a watan Oktoban bara.

Shi dai wannan mukamin na bukatar yardar daukacin mambobin wannan kungiyar kafin a tabbatarwa wanda aka zaba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG