Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ngozi Okonjo-Iweala Tana Kusantar Zama Shugabar WTO


Dr. Ngozi Okonjo-Iweala
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala

Tsohuwar minister kudi ta Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala tana kan hanyar zama darektar hukumar cinikayya ta duniya inda idan aka zabe ta, za ta zama mace da farko kuma bakar fata ta farko da zata rike wannan mukamin a tarihin kungiyar cikin shekaru 25 da kafa ta.

Wannan ya biyo bayan janyewa da ministar ciniki ta Koriya ta kudu Yoo Myung-hee ta yi a wata sanarwa da ta fitar yau jumma’a, inda ta bayyana cewa, ta tsaida shawarar janyewa daga takarar ne bayan tuntuba da tattaunawa da Amurka da kuma sauran manyan kasashe masu ikon fada a ji a kungiyar.

Janyewar da Yoo Myung-hee ta yi na iya taimakawa wajen ci gaba da farfado da yakin neman zabe da kuma kamala zaben sabon darekta da zai shugabanci kungiyar da tasirinta ke dishewa.

Yoo Myung-hee da Ngozi Okonjo-Iweala
Yoo Myung-hee da Ngozi Okonjo-Iweala

Rahotanni da nuni da cewa, jami’an gwamnatin Amurka da dama sun yi kira ga shugaba Joe Biden ya goyi bayan Okonjo-Iweala bayan da gwamnatin tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ta taka mata birki a shekarar da ta gabata. Abinda ya kawo saiko ga nasarar Okonjo-Iweala wadda a lokacin ta ke da goyon bayan sauran membobin kungiyar banda Koriya inda abokiyar takararta ta fito.

Wannan sanarwar ta dauki hankalin jama'a a kasashen duniya inda aka shiga yayata labarin a shafukan sada zumunta da kuma taya tsohuwar ministar murna . Tuni kafofin watsa labarai na duniya suka fara harsashen cewa, Okonjo-Iweala tana zata zama mace ta farko kuma bakar fata ta farko da zata shugabanci kungiyar.

Bayan jinjinawa abokiyar takatar ta Yoo Myung-hee da ta janye, Okonjo-Iweala ta ce tilas ne kungiyar WTO ta maida hankali kan shawo kan annobar Covid-19 da kuma farfado da tattalin arzikin kasashen duniya.

wto-dalilin-da-ya-sa-amurka-ba-ta-goyon-bayan-ngozi-okonjo-iweala

takarar-ngozi-okonjo-iweala-buhari-zai-shiga-kamfe

wace-ce-za-ta-zama-shugabar-wto-tsakanin-ngozi-okonjo-iweala-da-yoo-myung-hee

Ngozi Okonjo-Iweala mai shekaru 66 da haihuwa, banda rike mukamin ministar kudi a Najeriya har sau biyu, da ta taka rawar gani wajen taimakawa Najeriya fita daga basusuka da suka dabaibaye ta a wancan lokacin, ta kuma rike mukamin darekta a babban bankin duniya, da aikinta ya hada da kula da harkokin tattalin arzikin kasashen nahiyar Afrika a matsayin babbar darekta.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG