Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Iya Cimma Matsaya Da China Nan Ba Da Jimawa Ba - Trump


FILE - U.S. President Donald Trump, right, chats with Chinese President Xi Jinping in Beijing, China.

Kalaman na Trump na baya bayannan, suna zuwa ne, bayan da ya kara yawan haraji akan kayan China na kimanin dalar Amurka billiyan $200 da ake shigowa da su Amurka, kana da kara harajin akan kayan Chinar da suka kai na kimanin dala billiyan $300.

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka na iya cimma matsaya da kasar China a gobe, don warware rashin jituwar da ke tsakanin manyan kasashen mafiya karfin tattalin arziki a duniya, akan huldar kasuwanci.

Ya kuma zargi kasar China da cewa ita ce ba ta son bangarorin biyu su cimma matsaya.

A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yau Talata, shugaba Trump ya nuna cewa matakin da Amurka ta dauka a yanzu shi ne “matakin da ya fi dace wa fiye da duk matakin da za mu dauka.”

Ya kuma kara jaddada cewar karkashin mulkinsa, babu wata kasa da za ta sake kwarar Amurka, idan ana maganar kasuwanci.

Kalaman na Trump na baya bayannan, suna zuwa ne, bayan da ya kara yawan haraji akan kayan China na kimanin dalar Amurka billiyan $200 da ake shigowa da su Amurka, kana da kara harajin akan kayan Chinar da suka kai na kimanin dala billiyan $300.

Ita ma China ta rama da dora haraji akan kayan Amurka da ake shiga da su kasarta da suka kai na dala biliyan $60.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG