Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Iya Mayar Da Martanin Harin Da Aka Kai Wa Saudiyya


Yayin da duniya ke sauraron abin da zai biyo bayan harin da aka kai kan katafariyar matatar man Saudiyya dinnan, Amurka ta ce a shirye ta ke ta dau duk irin matakin martanin da Saudiyya ke so.

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce sojojin Amurka sun “kintsa da cikakkun makamai” don mayar da martani akan hare haren da aka kai a daya daga cikin matatun man Saudiyya mafiya girma, da kuma wurin da ya fi samar wa duniya danyan mai.

“Mu na da hujjar yin imanin cewa mun san wanda ya aikata," abin da Trump ya rubuta kenan ta kafar Twitter jiya Lahadi da yamma. Shugaban kasar ya kuma kara da cewa yana jira ya ji daga Saudiyya game da wadanda su ka yi imanin su suka shirya harin kuma “a bisa wane sharadi zamu dauki mataki.”
Tun da farko, Sakataran Harkokin Wajen Amurka, Mike Pompeo, ya wallafa wani sakon Twitter mai cewa “Yanzu Iran ta kaddamar da wani mummunan hari akan wurin da ake samar da makamashi a duniya," wanda bai yi la'akari da ikirarin 'yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran cewa su su ka kai harin da jirage marasa matuka ba.

Sai dai Iran ta kira zargin cewa ta na da hannu a harin da cewa "gagarumar karya ce."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG