Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Kan Bakarta Cewa Iran Ce Ta Kai Hari Kan Tankokin Mai


Amurka ta ce zata iya tabbatarwa jiragen ruwa dake kai-komo tsakanin tekun Peshan da tekun Oman babu wata matsalar sufuri kuma zata yi hakan ne ta hanyar diflomasiya ko kuma ta amfani da karfin soja, inda take ci gaba da kalubalantar Iran cewa itace ta kai hari a kan jiragen dakon mai a kan tekun.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fadawa shirin labaran Fox na jiya Lahadi cewa, ko shakka babu Jamhuriyar Islamiyar Iran ce ta kai wannan hari a kan jiragen ruwa ‘yan kasuwa da zummar hana jiragen ratsawa ta wurin.

Babban jami’in diflomasiyar na Amurka yace Amurka bata so wani yaki da Tehran, amma zata tabbatar da sufuri a kan hanyar dake hada yankuna tekun Peshan da tekun Oman, wani karamin yankin ruwan teku da jiragen raba mai ke amfani da su.

Iran ta musunta zargin da Amurka take mata cewa tana da hannu a cikin a harin da aka kaiwa jiragen Norway da Japan da suke dakon mai da wasu sanadarai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG