Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Ya Kawo Karshen Kwatanta Amfani Da Lafazin Sasanci A Manufofin Sa Kan Bakin Haure


Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Donald Trump, ya kawo karshen kwatanta amfani da lafazin sassauci a manufofinsa kan shigowar baki cikin Amurka, inda yake bayyana cewa zai mayar da Miliyoyin bakin da suka shigo ba bisa ka’ida ba, ya kuma jaddada aniyarsa ta gina katanga kan iyakar Amurka da Mexico, kuma yace Mexicon ce zata biya kudin ginin.

Trump dai ya bayyana kudurunsa kan bakin haure idan har ya lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a watan Nuwamba, shi da abokiyar karawarsa Hillary Clinton a wani jawabi da yayi ranar Laraba a jihar Arizona, a kokarin da Amurka ke yi na dakatar da kwararowar bakin haure daga Mexico da sauran kasashe.

Kafin wannnan jawabin nasa ne ya kai wata gajeriyar ziyara birnin Mexico City inda ya zanta da shugaban kasar Mexico, Enrique Pena Nieto kan batun bakin haure da sauran wasu batutuwa.

Jami’an Amurka sunyi imanin cewa akwai kimanin bakin haure Miliyan 11 da ke zaune a Amurka ba bisa ka’ida ba, kuma wannan shiri na Trump ka iya yin sanadiyar mayar da bakin hauren sama da Miliyan 6 zuwa kasashensu, haka kuma kusan Miliyan biyu ne suka aikata laifi a Amurka.

Akwai kuma mutane Miliyan 4.5 da suka shigo Amurka suka ki komawa bayan da visar su ta kare. Sai dai babu tabbacin ko me Trump zai yi ga bakin hauren da suka shigo kasar ba bisa ka’ida ba kuma basu aikata wani laifi ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG