Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Cafke Wadanda ta Zarga da Yunkurin Kifar da Gwamnatin Gambia


Yahya Jammeh, shugaban kasar Gambia

Hukumomi a Amurka sun zargi Njie da Faal da yunkurin kifar da gwamnatin Gambia makon jiya

Hukumomin Amurka sun cafke wasu ‘yan kasar biyu akan zargin suna da hannu a yukurin hambarar da gwamnatin Gambia da aka yi makon jiya. Su dai mutanen ‘yan asalin kasarta Gambia ne.

Ma’aikatar sharia tace an kulle Cherno Njie dan shekara 57 da kuma Papa Faal dan shekara 46 bayan an gurfanar dasu na wani dan lokaci a gaban sharia. An cafke Njie ne a Baltimore cikin jihar Maryland yayin da shi Faal ankamashi ne a Minneapolis a jihar Minnesota.

Ana zargin mutanen da karya dokar Amurka ta ‘yan babu ruwanmu da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.

Bayanai da suka fito daga ma’aikatar sharia sun nuna cewa Njie da Faal sun yi balaguro zuwa Gambia a watan jiya da nufin kifar da gwamnatin kasar.

Kafin su bar Amurka Faal da abokansa da suka hada baki tare sun sayi bindigogi da suka hada da manyan makamai wadanda suka tura zuwa Gambia da nufin yin anfani dasu wurin aiwatar da shirinsu.

Da a ce sun samu nasarar kifar da gwamnatin shugaba Yahya Jammeh ne to da shi Njie ne zai zama shugaban kasa na wujin gadi.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG