Jami'an Amurka sun ce sun wargaza wata makarkashiyar da al-Qa'ida ta kulla ta tarwatsa wani jirgin saman fasinja da ya doshi Amurka.

Hukumomi a Washington sun ce reshen kungiyar al-Qa'ida dake Yemen ta yi niyyar saka wani dan kunar-bakin-wake a cikin wani jirgin saman fasinjar da zai doshi Amurka dauke da nakiyoyin da zai boye a cikin kamfai, ko karamin wandonsa.

Suka ce an gano wannan makarkashiya aka kuma kama wannan bam da aka yi niyyar amfani da shi tun ma kafin wani jirgin sama ya fuskanci hatsari.

Majalisar tsaron kasa ta Amurka dake fadar shugaba ta White House ta fada cikin wata sanarwa jiya litinin cewa an fara fadawa shugaba Barack Obama wannan makarkashiya da aka bankado a cikin watan Afrilu, kuma tun daga lokacin ana yi masa karin bayani a kan halin da ake ciki game da ita. Sanarwar ta ce an tabbatarwa da shugaban cewa jama'a ba su fuskantar wata barazana daga wannan bam.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press yace wanda aka yi niyyar amfani da shi wajen kai harin yana kasar Yemen ne, kuma an shirya kai harin a lokacin da ake cika shekara guda da harin da Amurka ta kai ta kashe shugaban kungiyar al-Qa'ida, Osama bin Laden. Yace mutumin da yayi niyyar kai harin bai ma zabi wurin da zai kai ma harin ba, haka kuma bai ma sayi tikitin jirgin ba tukuna.