Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Kasar Pakistan Sun Yi Gangamin Tunawa da Osama Bin Laden


Magoya bayan jam'iyyar addini ta Jamiat-e-Ulema-e-Islam na rike da hoton hoton Osama bin Laden a yayin gangamin nuna kin jinin Amurka a birnin Quetta kasar Pakistan

Daruruwan 'yan kasar Pakistan sun yi dandazo a tituna albarkacin cikon shekara daya da mutuwar Bin Laden

Daruruwan ‘yan kasar Pakistan sun yi dandazo a kan tituna a yau Laraba albarkacin cikon shekara daya da mutuwar Osama Bin Laden shugaban kungiyar al-Qaida.

Ranar 2 ga watan Mayun shekarar 2011 jami’an tsaro Amurka na musamman su ka kashe bin Laden cikin wani harin boye da suka kai garin sojojin Pakistan na Abbottabad.

A birnin Quetta da ke kudu maso yammacin kasar, ‘yan jam’iyyar Jamiat-e-Ulema-e-Islam mai goyon bayan ‘yan Taliban ta yi tur da Allah waddai da kashe bin Laden, su na rera taken goyon bayan shugaban na al-Qaida kuma su na ta kona tutar kasar Amurka.

A garin Abbottabad kuma ‘yan makaranta ne su ka tururuwa a gurbin harabar gidan bin Laden, su na kiran neman zaman lafiya da kuma kawo karshen hare-haren da jiragen saman yakin Amurka ke kaiwa a cikin kasar Pakistan.

Gwamnatin kasar Pakistan ta yi tur da Allah wadai da hare-haren da kuma harin boyen da ya yi sanadin mutuwar bin Laden, wanda ta ce ya keta haddin kasar.

Kasar Pakistan na cikin hattara gagaruma, kuma an umarci dukkanin cibiyoyin tsaron kasar da kasancewa cikin maida hankali saboda yiwuwar samun hare-hare daga ‘yan tawayen da ke neman daukan fansar kisan da aka yiwa bin Laden.

A makon jiya ofishin jakadancin Amurka a Islamabad ya fada cewa daga ranar 27 ga watan Afrilu ya zuwa ranar 5 ga watan Mayu, ya bukaci ma’aikatan shi da su takaita zuwa wuraren cin abinci da kuma kasuwanni da ke Islamabad babban birnin kasar, sannan kuma ya shawarci Amurkawan da ke Islamabad da zama da su dauki irin wadannan matakai. Ofishin jakadancin bai bayar da dalilin yin kashedin tsaron ba, amma dai ranakun sun yi kicibis da cikon shekara daya da mutuwar shugaban al-Qaida Osama bin Laden.

XS
SM
MD
LG