Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Fara Raba Maganin Rigakafin Coronavirus A Fadin Kasar


Maganin Rigakafin Coronavirus
Maganin Rigakafin Coronavirus

Jiya Lahadi an fara jigilar sabbin alluran rigakafin coronavirus ta jiragen sama daga kamfanin hada magunguna na Pfizer dake garin Kalamazoo, na jihar Michigan, zuwa sassa da yankunan kasar Amurka.

Cikin hanzari za a fara allurar rigakafin Covid-19 daga ranar Litinin, a cewar Stephen Hahn, shugaban Hukumar Tantance Abinci da Magunguna ta Amurka, ya fada wa gidan talabijin na CNN. Zubin allurai fiye da 184,000 suna manyan motocin farko da suka bar wurin samar da allurar rigakafin na Pfizer.

Ma'aikatan kiwon lafiya da tsofaffi a cibiyoyin da ake kulawa da su na dogon lokaci, za su kasance a sahun farko na karbar zagaye na farko na allurai miliyan biyu da dubu dari tara, a daidai lokacin da ake ke ci gaba da samun masu kamuwa da cutar a Amurka.

Amurka ta fi kowace kasa yawan masu cutar coronavirus, inda kusan mutum 300,000 cutar ta kashe haka kuma fiye da mutum miliyan 16 cutar ta kama, a cewar Jami'ar Johns Hopkins.

Da yammacin ranar Jumma’a ne hukumar kula da abinci da magunguna ta FDA ta tabbatar da rigakafin da kamfanin Pfizer ya yi tare da takwararsa na kasar Jamus, BioNTech bisa bukatar gaggawa. Ma’aikatan kiwon lafiya da gidajen duban tsofaffi ne zasu fara samun maganin a cikin zubi miliyan uku na farko.

Shugaban hukumar abinci da maguguna Stephen Hahn ya fada a taron manema labarai a ranar Asabar a wajen Washington cewa zai sha allurar da zara an fitar da shi.

Hahn ya yaba wa aikin tabbatar da ingancin allurar inda ya ce shi ne mafi sauri a tarihin tabbatar da rigakafi a Amurka, ya kuma ce hukumar sa bata bada muhimmanci ga yin sauri a kan inganci ba.

XS
SM
MD
LG