Karamin ministan Muhalli na Najeriya, Alhaji Ibrahim Usman Jibrin, shine zai wakilci Najeriya a taron, yace dalilin da yasa Amurka ta gayyaci wannan taro shine kasancewa ruwa shine abin da yafi komai yawa a duniya, domin kashi Saba’in cikin ‘dari ruwa ne sauran kashi Talatin itace 'kasa a nan duniya, wanda ya hada da tekun Atlantic da tekun pacific da kuma tekun Indiya.
Dayawa dai an ta’allaka ne wajen amfani da Tekuna wajen safarar kayayyaki daga wani bangare na duniya zuwa wani, haka kuma mutane fiye da Biliyan Uku na dogaro ga teku wajen samun hanyar cin abincinsu. Hakan yasa aka kira wannan taro domin ganin cewa an gano wasu abubuwa dake kawo matsala kuma dole ne ayi maganinsu idan har ana son zaman lafiya a duniya.
Kasancewar Najeriya nada gaba na tekun Atlantic, kuma tana da manyan tashoshin jiragen ruwa tun daga Lagos har zuwa Port Harcourt da Calabar, a cewar karamin minista tabbas Najeriya ma na da matsala tunda ta kan tekunne ake shiga da fice na kayayyaki.
Domin karin bayani.