Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kai Hari Kan ISIS A Gabashin Syria


Shugaban Syria Bashar Assad
Shugaban Syria Bashar Assad

Har yanzu Amurka da kawayenta na cigaba da kai farmaki akan sansanonin kungiyar ISIS dake cikin kasar Syria da Iraq

Amurka tace ta kaddamar wani farmaki wanda "ya sami nasara". Ta auna harin ne kan mayakan ISIS a gabashin Syria, tareda sa ido kan shugabannin kungiyar.

Kakakin ma'aikatar tsaron Amurka keftin Jeff Davis, ya fada jiya Litinin cewa, an kaddamar da harin ne a lardin Deir Ezzor, wanda mayakan Amurka na musamman da aka azawa nauyin farautar shugabannin ISIS a Syria da Iraqi suka yi.

Bai bayyana ko su wanene aka auna harin kansu ba, sai dai yace an sami bayanan sirri masu yawa lokacin farmakin.

Kakakin na Pentagon yace, ikirarin da kungiyar da take kare hakkin BIl'Adam a Syria tayi cewa, an kashe mutae 25 lokacin harin, akwai kara gishiri a batun. Sai dai bai fadi yawan wadanda aka kashe a farmakin ba.

XS
SM
MD
LG