A yau Alhamis, shugaban kasar Iran, Hassan Rouhani ya kira matakin da Amurka ta dauka na kakaba takunkumi akan Ministan Harkokin Waje na Iran a matsayin "wasan yara."
A wani jawabi da ya yi wanda aka nuna a talabijin, Rouhani ya ce Amurka, ta yi ikrarin tana so ta hau teburin shawarwari da Iran ba tare da wasu sharudda ba, amma kuma sai ga shi ta sanya takunkumi akan Ministan Harkokin Wajen kasar.
“Wannan mataki ne da ba a saba gani ba,” a cewar wani babban jami’in gwamnatin Trump, a lokacin da yake tattaunawa kan matakin da Amurka ta dauka, akan ministan harkokin wajen na Iran, Mohammed Javad Zarif.
Umurnin takunkumin da Amurka ta sanya ya zargi Zarif da yin abubuwa a madadin jagoran kasar, Ayatollah Ali Khamenei, wanda kwanan nan aka sanya sa a jerin sunayen mutane na musamman da Baitulmalin Amurka ta sanyawa takunkumi aka kuma hana wani dan Amurka yin wata hulda da su.
Za ku iya son wannan ma
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum