Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kakabawa Rasha Sabbin Takunkumi


Gwamnatin Amurka ta kakabawa kasar Rasha wani sabbin takunkunmi a matsayin martini kan shisshigi da kuma satar bayanan da ake zargin Rasha ta yi a zaben shugaban kasar Amurka da aka yi a watan Nuwamba.

Jami’an sun ce Amurka za ta kori manyan jami’an leken asirin Rasha 35 daga kasar da kuma wasu hukumomin tattara bayanan sirrin kasar ta Rasha guda biyu.

Gwamnatin shugaba Obama na son ganin takunkumin ya fara aiki kafin ya bar mulkin, wato nan da ‘kasa da makonni uku.

Amma ma’aikatar harkokin wajen Rashan ta yi Allah wadai da yunkurin na kakaba mata sabbin takunkumi.

XS
SM
MD
LG