Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kara Kaimi A Tattaunawar Zaman Lafiya A Afghanistan


Sakataren Harakokin Wajen Amurka Mike Pompeo

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya fada ajiya Asabar cewa Amurka zata bada taimako a duk inda zata iya, yayin da yake ganawa da masu tattuanawa na bangaren gwamnatin Afghanistan a Qatar, a daidai lokacin ake ganin alamun samun nasarar cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban.

Ya ce “zan so na samu shawarwarin ku a kan yanda zamu karfafa yiwuwar samun sakamako mai cike da nsarar da muke baiwa juna,” inji Pompeo a lokacin da ‘yan jarida suka ji yana fadawa wakilan Afghanistan a tattaunawar.

Babban jami’in diflomasiyar Amurka mai barin gado ya kuma gana da wakilan Taliban a tattaunawar a Doha babban birnin Qatar, a lokacin da Amurka ke janye dakarunta daga Afghanistan cikin gaggawa biyo bayan mamaye kasar tun shekarar 2001.

Pompeo da wakilan Taliban sun tattauna a kan rage yawan tashin hankali a kasar da yaki ya daidaita, a cewar mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Cale Brown. Pompeo ya kuma bada kwarin gwiwar tattaunawa cikin gaggawa, domin samar da tsari a siyasance da zai kai ga ajiye makamai na dindindin a Afghanistan.

Taliban da gwamnatin Afghanistan sun fara tattaunawa a karon farko ne a cikin watan Satumba a birnin Doha bayan Amurka da Taliban sun sanya hannu a wata yaejejniya a cikin watan Faburairu. Amurka ta amince da janye dakarun kasar waje wadda a nata bangare Taliban tayi alkawarin samun tsaro da kuma bada himma ga tattaunawar.

Tun da safiyar Asabar ne Pompeo ya gana da yarima mai jiran gado na Hadaddiyar Daular Larabawa, Yarima Mohammed bin Zayed Al Nahyan a birnin Doha kana suka tattauna a kan kyautata alakara Daular Larabawan da Isra’ila, a wani matakin martani ga tasirin Iran a Gabas ta Tsakiya da kuma bukatar cimma zaman lafiya a Yamal ta hanyar siayasa, a cewar ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

Sakataren ya kuma gana da shugaban Qatar Emir Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani a Doha tare da karamin firai minister da kuma ministan harkokin waje.

Ziyarar da Pompeo ya kai a Qatar tana cikin rangadin kwanaki goma da ya yi a baya bayan nan a kasashe bakwai a Gabas ta Tsakiya da Turai, yayin da gwamnatin shugaba Donald Trump ke shirin barin gado.

XS
SM
MD
LG