Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Maido Da Tallafin Tsaro Ga Ukraine


Ziyarar Sakataran Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio Zuwa Jeddah
Ziyarar Sakataran Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio Zuwa Jeddah

Bayan kusan sa’o’i takwas ana tattaunawa, Ukraine ta sanar da shirinta na amincewa da shawarar Amurka na tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30, a yakin da take yi da Rasha, yayin da take jiran amincewar Kremlin.

Nan take gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump za ta dage takunkumin dakatar da raba bayanan sirri da kuma dawo da taimakon tsaro da take ba Ukraine bayan tattaunawar da manyan jami’an Amurka da na Ukraine suka yi ranar Talata a birnin Jedda na kasar Saudiyya.

A halin da ake ciki, ana sa ran jami’an Amurka za su tattauna da jami’an Rasha cikin kwanaki masu zuwa. Rahotanni sun ce, wakili na musamman da Trump ya nada, Steve Witkoff, na shirin ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow cikin wannan makon.

Bayan kusan sa’o’i takwas ana tattaunawa, Ukraine ta sanar da shirinta na amincewa da shawarar Amurka na tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30, a yakin da take yi da Rasha, yayin da take jiran amincewar Kremlin.

A ranar 5 ga watan Maris da ya gabata, Trump ya dakatar da bai wa Ukraine bayanan sirri, matakin da ake kallo a matsayin wani yunkuri na nuna matsin lamba ga shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy kan tattaunawa da Rasha don kawo karshen yakin da aka shafe shekaru uku ana fafatawa.

Nan take dai Fadar Kremlin ba ta ce komai ba kan shawarar tsagaita wuta daga Amurka da Ukraine.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Rasha ta ce kawai tattaunawa tare da jami’an Amurka za ta iya gudana a cikin wannan makon.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio da mai ba da shawara kan tsaron Amurka Mike Waltz ne suka jagoranci tawagar Amurka a birnin Jedda a daidai lokacin da Trump ke kokarin ganin an kawo karshen yakin da aka fara a farkon shekarar 2022 da Rasha ta mamaye Ukraine.

Zelenskyy bai halarci taron na ranar Talata ba, inda Ukraine ta samu wakilcin shugaban ma’aikatan Zelenskyy, Andriy Yermak, Ministan Harkokin Waje Andrii Sybiha, Ministan Tsaro Rusterm Umerov da kuma kwamandan soji Pavlo Palisa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG