Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tasa Kyeyar Wata 'Yar Mexico Zuwa Kasarta


Masu gwagwarmaya da korar bakin haure a jihar Arizona

Amurka ta tusa kyeyar wata mace uwar‘ya’ya biyu wadanda ‘yan kasa ne zuwa Mexico jiya Alhamis, kamar yadda lauyan ta ke cewa, wannan mataki ya nuna canji ga manufofin Amurka dangane da bakin haure.

Lauya Ray Maldonado, yace an tsare ta tun ranar Laraba a Phoenix jahar Arizona, sailin da ta je ofishin shige da fice kamar yadda ta saba yi.

Lauya Madonado yace karamin ofishin jakadancin Mexico ne ya sanar dashi cewa wannan matar da yake baiwa kariyar shara’a an mayar da ita gida Mexico.

Ita dai wannan baiwar Allah, ‘yar shekaru 36 da haihuwa mai suna Garcia de Rayos, tasha gitta wurin jami’an shige da fice na Amurka tun daga shekarar 2008 lokacinda ta shiga hannutana anfani da katin nan dake kunshe da bayanan maishi da ake kira social security, na bogi, saiilin wani samamen da jami’an tsaro suka kai a wajen aikin ta. Abunda aka saba shine tana kai kanta ofishin akai akai inda take amsa tambayoyi sannan a kyale ta.

Sai dai wannan karon bata sha da dadi ba domin ko a ranar Laraba sailin da Royos taje ofishin, sai aka kame ta kuma nan take aka fara shirya takardun mayar da ita kasar su duk ko da yake ta kwashe sama da shekaru 22 a nan Amurka.

Sai dai lauyan nata yace tuni ya gabatar wa kotu bukatar dakatar dawannan yunkurin na mayar da ita gida Mexico.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG