Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma'aikatar Shari'ar Amurka Ta Daukaka Kara Akan Dakatar da Dokar Shugaba Trump


Shugaban Amurka Donald Trump wanda ya kafa dokar hana shigowar baki daga wasu kasashen musulmi bakwai

Ma'aikatar Shari'ar Amurka ta gabatar da takardar daukaka kara a kotun daukaka kara ta tarayya da ke San Francisco, ta bukatar maido da umurnin Shugaba Donald Trump na hana shigowa Amurka mutanen wasu kasashe 7 masu rinjayen Musulmi.

Kotunan Daukaka Karar, na shirin fara sauraron muhawarar baka daga bangarorin biyu a yau dinnan Talata.

Takardar Daukaka Karar ta Ma'aikatar Shari'ar na cewa hana shigowar, 'Wani iko ne da Shugaban kasa ke da shi na hana baki shigowa Amurka da kuma shigar da 'yan gudun hijira." Takardar ta bayyana umurnin da wani alkalin tarayya ya bayar na janye umurnin hana shigowar da cewa wani kuskure ne, kuma ya wuce makadi da rawa.

Wasu lauyoyin Amurka da kanfanoni kusan 100 da wasu jahohi biyu da wasu 'yan jam'iyyar Democrats ciki har da Sakatarorin Harkokin Waje na da John Kerry da Madeleine Albright sun kalubalanci wannan dokar hana baki shigowa a kotu.

'Yan jam'iyyar Democrat na zargin cewa an bayar da umurnin hanin ne da abin da su ka kira, "muguwar manufa, kuma ba a aiwatar cikin tsari ba, kuma ba wani bayyani kwakkwara."

Baya ga haka, kamfanonin fasaha ciki har da manya-manya da ke Silicon Valley irinsu Apple, da Facebook, da Google, Microsoft da Twitter, sun gabatar da kara ranar Lahadi a kotun ta daukaka kara, su na masu goyon bayan karar da aka gabatar ta neman a soke dokar hana shigowar.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG