Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta Tura Jami'an Sojojinta Zuwa Somalia, a Karo na Farko Cikin Shekaru 20

A wanan hoto wasu sojojin Amurka ne da takwarorinsu na Uganda a karshen wani rawan daji da aka shirya a yankin a 2011.
A wanan hoto wasu sojojin Amurka ne da takwarorinsu na Uganda a karshen wani rawan daji da aka shirya a yankin a 2011.

Rundunar sojojin Amurka tace ta tura wata karamar tawagar jami’anta masu bada shawara zuwa Somalia, wannan ne karo na farko da Amurka zata yi haka tun a farkon wajajen shekarun 1990.

Rundunar sojojin Amurka tace ta tura wata karamar tawagar jami’anta masu bada shawara zuwa Somalia, wannan ne karo na farko da Amurka zata yi haka tun a farkon wajajen shekarun 1990.

Wani kakakin rundunar Amurka mai kula da Afirka, kanal Tom Davis, ya fada jiya jumma’a cewa an kafa tawagar tun cikin watan oktoba, amma sai a cikin watan jiya ne ta fara aiki. Jami’an Amurka suka ce dududu sojoji biyar ne a cikin tawagar mashawartan.

Rabon sojojin Amurka a Somalia tun farkon 1994. Watanni bayanda aka harbe jiragen yakinAmurka biyu masu saukar ungulu samfurin BlackHawaka karshen shekara ta 1993, aka kashe Amurkawa 18.

Davis yace aikin sojojin shine bada shawarwari ga sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar hada kan kasashen Afirka a Somalia, da kuma jami’an tsaron Somalia.

Sojojin Somalia da kuma masu aikin kiyaye zaman lafiya na tarayyar Afirkan suna fafatawa da kungiyar al-shabab mai alaka da al-Qaida. Dakarun kasar sun wkace babban birnin kasar Mugadishu a shekarar 2011, duka da haka kungiyar tana ci gaba da kai hare hare lokaci lokaci kan birnin.

Haka kuma kungiyar al-shabab ta dauki alhakin kai hare hare a wajen kasar, da suka hada harda hari da aka kai kan katafaren kasuwar zamani a birnin Nairobi na kasar Kenya cikin watan satumban bara,mautane masu yawan gaske suka halaka a harin.
XS
SM
MD
LG