Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta umarci iyalan sojojinta su fice daga kudancin Turkiya


Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter

Amurka ta umarci iyalan sojojinta su fice daga wadansu sassan kudancin Turkiya bisa dalilan tsaro.

Ma’aikatar tsaron Amruka ta bada umarnin sakewa iyalan sojoji dari shida da saba’in matsuguni daga sansanin mayakan sama na Incirlik da Mugla.

Sakataren ma’aikatar tsaro Peter Cook yace ba wata barazana ta sa aka dauki wannan matakin ba, sai dai an yi haka ne a matsayin rigakafi.

Umarnin bai shafi iyalan sojoji dubu dari dake sansanan Ankara da Istanbul ba.

Sanarwar ta zo sa’oi bayanda mai ba fadar shugaban kasa ta White House shawara akan harkokin tsaro Susan Rice da sakataren ma’aikatar harkokin wajen Amurka John Kerry suka gana da ministan harkokin kasashen ketare na kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu. Sai dai, wani jami’in tsaro ya shaidawa Muryar Amurka cewa, lokacin ya yi karo da juna ne kawai.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG