Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yaba Da Bayannan Sirri Da Israila Ta Samu Akan Iran


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Mike Pompeo da Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Fadar White House tana yabawa kasar Israila akan bayanan sirri da ta samu akan shirin nukiliyar kasar Iran da suka nuna Iran ta keta yarjejeniyar da aka cimma da ita a shekarar 2015

Fadar White House ta shugaban Amurka tana yabawa sabbin bayanan sirri da Isra'ila ta samar dangane da shirin Nukiliyar Iran,ta kira bayanan "sabo kuma gamsarwa" abunda kawai jami'an Amurka basu yi ba, shine su fito su ce hukumomi a Tehran da laifin keta yarjejeniyar da kasar ta kulla da manyan kasashen duniya a shekara ta 2015.

Dazun nan Jami'an Amurka da suka duba kasidun da feya-feyan vidiyo da jami'an leken asirin Isra'ila suka samu, sun ce kasidun bisa dukkan alamu sahihai ne, kuma sun tafi dai dai da bayanan da Amurka ta tattara cikin shekaru da suka wuce.

Sakatariyar yada labarai a fadar White Saraha Huckerbee Sanders tace, bayanan sun nuna cewa Iran tana kan kudurin kera makamai masu linzami da zasu iya goyon makaman kare dangi.

Tun farko a jiya Litinin Firayi ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zargi Iran da yin karya a kan ayyukanta na kera makaman nukiliya da take ci gaba dashi, wanda ya sabawa yarjejeniyar kasa da kasa ta shekarar 2015 da ta haramtawa Tehran din shirin nukiliya.

Sai dai babu martani da Iran ta bayar nan da nan a kan jawabin Netanyahu. Amma kafin nan, ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya maida batun abin dariya, yana mai cewar, yaron nan mai yawan koke-koke ya sake yi. Yace akwai iyakar iya wasa da hankali wasu mutane a wasu lokauta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG