Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Alwashin Kama China Da Alhakin Amfani Da Fitilun Lasers


Wasu Sojojin Amurka yayin wata atusaye a watan Afrilun 2018.

A wani takaitaccen bayani da suka saki, ma’aikatar sojojin China tace wannan zargi ba gaskiya bane.


Mai Magana da yawon sojin Amurka Dana White, ta ce manyan fitilun lasers din an harbosu ne daga daga wani sansanin sojin dake garin Doraleh kusan sau 3 in da ya haifar da ciwuka a idanunwan matukan jirgin saman Amurka guda 2.


"Wannan aika-aika tana zama barazana ga sojojin saman mu. Mun kalubalanci gwamnatin China sannan mun bukaci su bincika abubuwan da suka faru," inji White.


Jami’an ma’aikatar tsaron Amurka sun gargadi ci gaban amfani da wannan fitilun lasers da cewa, za su iya cutar da matukan jiragensu sannan su zama barazana ga zagayen su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG