Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Yi Gargadin Cewa Akwai Yiwuwar Ta Sake Kai Hari


Shugaban Kasar Aurka Donald Trump
Shugaban Kasar Aurka Donald Trump

Amurka ta kare hare haren da ta kai ta sama a ranar Lahadi da ta auna mayakan da suke samu goyon bayan Iran a Iraqi da Siriya, ta kuma yi gargadin cewa za ta iya sake kai wani harin, duk da irin sukar da jami’an Iran suka yi da kuma wata sabuwar barazana daga mayakan da kan su.

“Ba zamu bari Iran ta sha ba na yin amfani da wasu mayaka don su kai hari akan muradun Amurka,” wani babban jami’in ma’aikatar harkokin wajan Amurka ya fadawa manema labarai jiya Litinin, yana bayyana hare haren a matsayin na kariya.

Hare-haren Amurkan ya auna wajan ajiye makaman kungiyar Kataeb Hezbollah da inda suke bada umarni ga sauran wurare a Iraqi da kuma gabashin Siriya, da ya hallaka akalla mutane 25 kana ya jirkata wasu da dama.

Sai dai Amurka ta ce hare haren saman mayar da martani ne ga harin roka a sansanin sojan Iraqi a ranar juma’a da ta gabata, wanda ya hallaka ma’aikacin kwantiragin ma’aikatar tsaron Amurka.

Harin dai ya janyo bacin rai da kuma suka daga manyan jami’in Iraqi.

A ranar Litinin, Firai Ministan Iraqi Adel Abdul Mahdi ya yi Allah wadai da hare haren, yay I kuma gargadi a cikin kalamansa cewa matakin na Amurka ba zasu yarda da shi ba kuma akwai mummunan sakamako.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG