Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka tace Koriya Ta Arewa Ba Abokiyar Gabarta Ba Ce


Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rex Tillerson

Babban jakadan Amurka, sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson yana aikawa Koriya ta Arewa, sakonnin cewa "Amurka ba makiyar ta ba ne.

Kalaman nasa na zuwa ne a yayinda fadar White House take cewa, bata dauke komi ba cikin jerin matakai da take da su na takawa shirin makamai masu linzami da na Nukiliya da kasar take yi burki.

A taro da manema labarai da ma'aikatar harkokin wajen Amurka take yi kullum na jiya Talata, sakataren a wani mataki na ba kasafai ba, yace "Amurka bata neman canjin gwamnati a koriya ta Arewa, bata bukatar ganin rugujewar gwamnatin, bata ma neman a gaggauta hadewar kasashen ko zirin cikin gaggawa ba, hakan bata nema wata hujja da zata bamu damar tura sojojin mu cikin kasar ba."

Duk da furucin da sakatare Tillerson yayi cewa "Amurka bata lamunta da barzanar da koriya ta Arewa take mata ba," yace "muna fata a wani lokaci nan gaba, zasu fara fahimtar hakan, kuma zamu zauna mu tattauna da su."
Amma akwai alamun hakurin wasu wakilan majalisun dokokin Amurka ya fara kaiwa wuya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG