Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Yau za'a fara zaben fidda gwani na zaben shugaban kasa a jihar Iowa


'Yan takaran bangaren jam'iyyar Democrats
'Yan takaran bangaren jam'iyyar Democrats

A bayan da aka shafe wata da watanni ana gangami da tarurruka da lacvcoci da hawa kan durum, yau litinin za a kaddamar da kakar zabubbuka da tarurrukan tsayar da ‘yan takara a babban zabe na Amurka, inda masu jefa kuri’a na Jihar Iowa zasu gudanar da tarurruka a unguwanni domin zaben wadanda suke son su tsaya musu takarar shugaban kasa. . A bangaren ‘yan Republican, attajiri Donald Trump ya bayar da rata marar yawa ma sanata Ted Cruz daga Jihar Texas, wanda alamu suka nuna cewa yayi tuntube a lokuta da dama kafin wannan zabe na yau. A bangaren ‘yan Democrat kuwa, zaben kusan ya zamo na kan mai uwa da wabi a tsakanin tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton, da sanata dan Indipenda daga Jihar Vermont, Bernie Sanders, wanda ya ayyana kansa a zaman dan Democrat mai ra’ayin gurguzu. Masu kwadayin tsayawa takarar sun karade jihar ta Iowa jiya lahadi, suka gudanar da tarurruka a kowane lungu na jihar, tare da caccakar lamirin abokan adawarsu.

Kafin wannan muhimmin zabe na farko a kakar zaben ta bana, kuri’un neman ra’ayoyin jama’a a jihar ta Iowa sun nuna cewa a tsakanin manyan jam’iyyun Republican da Democrat, babu wani fitaccen gwani, inda ‘yan bana-na-shigo a harkokin siyasar jam’iyyun biyu suke ci gaba da nuna kasaita.

Kafin wannan muhimmin zabe na farko a kakar zaben ta bana, kuri’un neman ra’ayoyin jama’a a jihar ta Iowa sun nuna cewa a tsakanin manyan jam’iyyun Republican da Democrat, babu wani fitaccen gwani, inda ‘yan bana-na-shigo a harkokin siyasar jam’iyyun biyu suke ci gaba da nuna kasaita.

A bangaren ‘yan Republican, attajiri Donald Trump ya bayar da rata marar yawa ma sanata Ted Cruz daga Jihar Texas, wanda alamu suka nuna cewa yayi tuntube a lokuta da dama kafin wannan zabe nay au.

A bangaren ‘yan Democrat kuwa, zaben kusan ya zamo na kan mai uwa da wabi a tsakanin tsohuwar sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton, da sanata dan Indipenda daga Jihar Vermont, Bernie Sanders, wanda ya ayyana kansa a zaman dan Democrat mai ra’ayin gurguzu.

Masu kwadayin tsayawa takarar sun karade jihar ta Iowa jiya lahadi, suka gudanar da tarurruka a kowane lungu na jihar, tare da caccakar lamirin abokan adawarsu.

'Yan takaran bangaren Republican
'Yan takaran bangaren Republican

XS
SM
MD
LG