Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta 'Dagewa Sudan Takunkumi


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Gwamnatin shugaba Obama ta ce za ta dage wasu takunkumi hada-hadar kudade da ta kakabawa Sudan, kamar yadda wani babban jami’in gwamnti ya fada jiya Alhamis.

A yau Juma’a ake sa ran Fadar shugaban kasa ta White House za ta bayyana wannan mataki da take shirin dauka.

Amurkan ta cimma wannan matsaya ce, bayan gamsuwa da ta fara nunawa game da matakan da Sudan ke dauka wajen yaki da ayyukan ta’addanci da rage yawan fadace-fadace da hana mafaka ga ‘yan tawayen Sudan ta Kudu da kuma kyautata hanyoyin gudanar da ayyukan jin-kai ga masu bukata.

A shekarar alif-dari-tara-da-casa’in-da bakwai, Amurka ta fara kakaba takunkumi akan Sudan, ciki har da na kasuwanci da kuma dakile wasu kadarorinta, saboda take hakkokin bil’adama da kuma ayyukan ta’addanci.

Sannan a shekarar 2006, Amurkan ta sake sakawa kasar wasu takunkumi saboda abinda da ta kwatanta a matsayin sa hanu a fadan Dafur.

XS
SM
MD
LG