Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dauki Matakin Farko Na Soke Tsarin Kiwon Lafiya Na Obamacare


Wasu masu zanga-zangar neman a soke tsarin kiwon lafiya na Obamacare

Jami’iyar Republican ta kasar Amurka da ke da rinjayi a majalisar kasar, ta dauki matakin farko na soke shirin kiwon lafiya na shugaba Barack Obama.

‘Yan Jami’iyar Republican suna lashi takobin soke dokar shirin kiwon lafiya da ake kuma kira Obamacare, da zarar shugaba mai jiran gado Donald Trump ya kama aiki.

Majalisar ta kada kuri'a yau Alhamis a kan soke wannan doka inda masu ra’ayin soke dokar suka samu kuri'u 51 a kan kuri’u 48 na wadanda suke ra’ayin a kyale dokar, wannan karamin rinjayi ba zai ba yan Democrat damar takawa daukar wannan mataki birni ba.
Republican itace take da wakilai 52 cikin wakilai dari na majalisar dattawa.

A majalisar wakilai kuma inda har iyau Republican ke da rinjayi, ana saran zata kada kuri’a a kan wargaza wannan shirin kiwon lafiya a wannan mako.
Shugabannin na Republican suna shirin tsara kudurin wannan dokar da suke kokarin fidda shi kafin karshen watan Janairu.

Babban tamabaya itace, mai zai faru idan Republican ta yi nasarar wargaza wannan shiri. Kawo yanzu bakin jam’iyar Republican bai zo daya ba, kan shirin maye gurbin wannan shirin kiwon lafiya da yake ba Amurkawa miliyon 20 inshoran kiwon lafiya, wadanda a da basu da inshora.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG