Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Fice Daga Syria - Trump


Amurka ta ce “za ta fice” baki daya daga Syria, domin kaucewa ci gaba da zub da jinin da ake yi da bata dukiyoyi a kasar ta Syria, wacce yakin basasa ya daidaita, tun da an riga an yi galaba akan mayakan ISIS da suka ayyana kasar a matsayin daularsu.

Shugaban Amurka Donald Trump ne ya bayyana matsayar a jiya Laraba, yana mai cewa, lura da shirin tsagaita wuta da aka cimma tsakanin Turkiyya da mayakan Kurdawa da Amurka ke marawa baya a arewa maso gabashin Syria na ci gaba da gudana, lokaci ya yi da za a bar wa wasu dawainiyar samar da zaman lafiya a kasar.

A ranar Talatar da ta gabata, Turkiyya ta ce, ba ta ga dalilin da zai sa ta ci gaba da kai hare-hare akan Kurdawan ba, bayan da Amurka ta sanar da ita cewa, Kurdawan sun janye a yankin, lamarin da ya sa, Shugaba Trump ya dage takunkumin da ya kakabawa Turkiyya dalilin kai hare-haren.

Shugaba Trump ya ce, “na ba Sakataren baitul malin Amurka umurnin ya dage takunmin da aka sakawa Turkiyyar a ranar 14 ga watan nan, sai dai idan har wani abu na akasi ya gitta.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG