Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Yi Taron Karfafa Diflomasiyya Da Cinikayya Da Ghana a Accra


Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo

A ranar goma sha shida ga watan Yuni ne ake sa ran Amurka zata gudanar da wani taron karfafa hadakar diflomasiyya da cinikayya tsakaninta da Ghana.

ACCRA, GHANA - Matakin zai ba Afirka damar cimma nasarar inganta yarjejeniyar cinikayya mara shinge tsakanin kasashen nahiyar Afrika wadda ake kira Continental Free Trade Agreement da turanci.

Taron da za a gudanar a Accra babban birnin kasar Ghana zai samu halartar mataimakin sakataren harkokin bunkasa ci gaban kasuwanci na Amurka Donet Dominic Graves, da ministan tattalin arzikin kasar Ghana Ken Ofori Attah, da kuma wasu jami’an gwamnatocin kasashen biyu.

Taken wannan taron shi ne karfafa yarjejeniya a kasashen Afirka domin bunkasa harkar kasuwanci tsakaninsu da Amurka.

Masana sun ce taron zai bai wa shalkwatar AFCFTA da ke Accra damar mu'amala da al'ummar Afrika da ke zama kasashen ketare, da masana'antu masu zaman kansu, da masu zuba jari domin ganin an inganta yarjejeniyar ba tare da wata matsala ba.

Batun da zai fi daukar hankali a taron shi ne harkar kwastam da samar da kayan aiki, da sarrafa kayayyakin ta hanyar amfani da na’ura tare da amfani da fasahar zamani don karfafa tattalin arziki mai dorewa a Afirka.

Kafin karshen taron ana sa ran karfafa hadakar kasuwanci tsakanin Amurka da nahiyar Afrika musamman fannin zuba jari, abinda zai taimaka sosai wajen inganta yarjejeniyar ta cinikayya mara shinge a Afirka da walwalar tafiye-tafiye.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adam:

Amurka Za Ta Yi Taron Karfafa Diflomasiyya Da Cinikayya Da Ghana a Accra
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

XS
SM
MD
LG