Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Japan Ta Lallasa Ghana 4-1 A Wasan Sada Zumunta


Dan wasan Ghana Jordan Ayew (AP)

Dan wasan Ghana Jordan Ayewa ne ya zura kwallo daya tilo da Ghana ta samu.

Japan ta doke Ghana da ci 4-1 a wasan sada zumunta da suka buga a birnin Kobe da ke kasar ta Japan.

Kamar Ghana, ita ma Japan ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar.

Japan ta samu kwallayenta daga dan wasa Miki Yamane, Kaoru Mitoma, Takefusa Kubo da Daizen Maeda kamar yadda AP ya ruwaito.

Dan wasan Ghana Jordan Ayewa ne ya zura kwallo daya tilo da Ghana ta samu.

A ranar Talata Japan za ta kara da Tunisia yayin da Ghana za ta fafata da Chile a wasu wasannin sada zumunta da aka shirya za a yi.

A ranar 21 ga watan Nuwamba za a fara gasar ta cin kofin duniya a Qatar.

Dubi ra’ayoyi

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG