Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Fitar da Tsarin Tattaunawar Zaman Lafiyar Gabas ta Tsakiya


Pence da Netanyahu
Pence da Netanyahu

Amurka ta fada a jiya Talata cewa, kafin karshen wannan shekara zata fidda tsarin tattaunawar zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya, sai dai mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence yace hakan zai ta’allaka ne a kan amincewar Falasdinu ta koma kan teburin tattaunawa da Isra’ila.

A lokacin da ya kamala ziyararsa ta kwanaki uku da ya kai a Gabas ta Tsakiya, Pence ya fadawa kampanin dillancin labarai na Reuters cewa, fadar White House tana tattaunawa da kawayenta na yankin ko zasu iya fitowa da tsarin tattaunawar zaman lafiyar. Amma dai hakan zai tabbata ne bisa amincewar Falasdinu na komawa ga teburin tattaunawar.

Wani babban jami’in Fadar White House ya fadawa manema labarai a birnin Kudus cewa, masu tattaunawa na bangaren Amurka basu kayyade lokacin kamala tattaunawar ba, saboda a baya cimma lokacin da aka kayyade ba.

Bangarorin zasu dace a kan lokacin da suka amince su fara tattauanawar, inji jami’in na White da ya bukaci a sakaya sunansa.

Pence ya fada a hirarsa da Reuters cewa, shi da shugaba Donald Trump, sun yi imanin shawarar dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus zai taimaka ainun wurin cimma tattaunawar zaman lafiyar yankin.

Facebook Forum

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG