Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Halarci Taron Kasuwani A Saudiya-Inji Sakatren Bitalmlin Amurka


Steve Mnuchin
Steve Mnuchin

Sakataren bitalmalin Amurka Steve Mnuchin, ya fada a jiya Juma’a cewa yana kan bakarsa na halartan babban taron zuba jari a kasar Saudi Arabi a karshen wannan wata, duk da tarin shaidar dake nuna an kashe dan jaridar Saudiyar a ofishin jakadancin Saudi Arabia a Istanbul a Turkiya.

Mnunchin ya fadawa telbijin CNBC cewa yana ci gaba da shirinsa na halartan taron. Yace idan wani abu ya biyo bayan haka, ko kuma an samu wata sakiya, zai yi nazari akai, amma dai yana kan batun zuwa taron.

Wasu manyan bankuna a dandalin hada hadar kasuwancin duniya na Wall Street, zasu halarci wannan babban taron kasuwanci a birnin Riyadh, duk da cewar wasu manyan kamfanonin yada labarai da manyan 'yan kasuwa sun janye daga halartan taron, kana suka daina huldan kasuwanci da yankin Gabas ta Tsakiya.

Hamshakin dan kasuwar Birtaniyan nan Richard Branson ya fada a jiya Juma’a cewa zai dakatar da tattaunawarsa a kan taron zuba jarin na Saudi Arabia a kamfaninsa na Virgin Groups.

Wasu manyan 'yan kasuwa kamar Steve Case daya daga cikin masu kamfanin kasuwancin yanar gizo AOL, da mai kamfanin sufuri na Uber Dara Khosrowshahi da Robert Bakish mai kamfanin Viacom, duk sun ce ba zasu halarcin taron na Riyadh ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG