Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Sayarwa Da Iran Jiragen Daukar Fasinja


Amurka ta ba kamfanin Airbus izini ta sayarwa Iran jiragen fasinja guda 17, a wata babbar kwangila ta kimanin Dala Miliyon 25.

Wannan cinikin tun cikin watan Janairun da ya wuce aka so a kamalla shi amma ba a iyakamalawa ba, sai bayan da aka rattaba hannu akan yarjejeniyar da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran dangane da kokarin kasar na neman makamashin nukiliya .

An dage takunkumin dake hana kampnoni su yi kasuwanci da Iran kamar kampanin Airbus biyo bayan amincewar da Iran din tayi na wargaza shirin nukiliyarta amma duk da haka kampanonin Turai suna bukatar amincewar Amurka kafin daddale wannan cinikin da Iran.

XS
SM
MD
LG