Accessibility links

Amurka Zata Taimakawa Najeriya Tayi Zabe Lafiya


Jakadan Amrka a Najeriya tare da John Kerry Sakataren Harkokin Wajen Amurka

Gwamnatin Amurka zata taimakawa Najeriya tayi zabe mai adalci da gaskiya

Jakadan Amurka a Najeriya Mr Geofrey Hopkins shi ya tabbatar da hakan yayin da ya kai ziyara jihar Oyo.

Jakadan yace yana da matukar mahimmanci a yi zabe mai adalci da gaskiya, wato jama'a su zabi wadanda suke so a kuma tabbatar da abun da suka zaba. Yin hakan zai habbaka mutuncin Najeriya da 'yan Najeriya a idanun duniya.

Yayin da yake yiwa jakadan maraba gwamnan jihar Sanata Ajimobi ya bukaci kasar Amurka da ta taimakawa Najeriya a wajen harkokin tsaro da tattalin arziki. Gwamnan yace dama kasar Amurka ta dade tana takarawa domin harkokin siyasa a Najeriya.

Gwamnan ya sake kiran Amurka ta agazawa jiharsa domin tattalin arzikinta ya bunkasa.

Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal.

XS
SM
MD
LG