Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janaral Buhari Zai Kawo Karshen Boko Haram da Cin Hanci da Rashawa


Janaral Muhammad Buhari.
Janaral Muhammad Buhari.

Yayin da yake jawabi a gangamin neman zabe da yayi a Taraba Janaral Buhari ya saba layar yakar muggan abubuwan da suka addabi kasar.

Yace gwamnatinsa zata kawo karshen Boko Haram, cin hanci da rashawa da kuma rashin aikin yi.

Abubuwan da suka addabi Najeriya musamman tashin tashinar Boko Haram basu fi karfin Najeriya ba amma suna cima kasar tuwo a kwarya. Ya kira masu goyon bayansa su yi zabe amma su tsare kada su kuskura su bari PDP tayi magudi.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana cikin wadanda suka raka Janaral Buhari zuwa gangamin Taraba. Da yake jawabi Atiku ya waiwayi baya lokacin da suke jihar Gongola da Adamawa kafin a kirkiro jihar Taraba. Yace bai taba kawo masu dan takarar da ba'a zabeshi ba. A wannan karon ya kawo masu Janaral Buhari su zabeshi.

Ita ma 'yar takarar kujerar gwamnan jihar ta Taraba a karkashin tutar APC tace ranar gaskiya ta zo. Jama'a da yawa ne suka yi cincirindo wurin gangamin.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

XS
SM
MD
LG