Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Sun Mallaki Bindigogi Fiye Da Al'ummar Kowace Kasa


Bindigogi
Bindigogi

Kungiyar dake kidigdigar wadanda suka mallakar makamai dake da cibiyarta a Geneva ta gano cewa Amurkawa suka fi al'ummar kowace kasa a duniya yawan wadanda suka mallaki makamai, fiye da China ko India saboda kashi arba'in na duk makaman dake hannun fararen hula a duniya suna Amurka ne

Wani sabon rahoto da wata kungiyar dake kidigdigar wadanda suka mallaki makamai da cibiyar ta ke birnin Geneva, ya gano cewa farar hula anan Amurka sun mallaki bindiga fiye da kowace kasa, domin kusan kashi arba’in daga cikin dari na bindiga da aka kiyasta sun kai miliyan dari takwas da hamsin da bakwai suna hannun farar hula ne.

Rahoton da aka gabatar jiya Litinin yace Amerikawa sun mallaki bindiga miliyan dari uku da casa’in da uku fiye da dukan kasashe ashirin da biyar da mutane suka fi yawan mallakar bindiga.

Idan aka kwatanta da kasashen Indiya da China wadanda kowacen su take da kimamin mutane biliyan daya da miliyan uku, to amma su ne suka zo na biyu da na uku akan yawan farar hula wadanda suka mallaki bindiga, miliyan saba’in da kuma kusan miliyan hamsin.

Batun kayade mallakar bindiga batu ne da ake ta muhawar akan sa a siyasance a nan Amurka bayan da aka yi ta samun mutane suna harbe harben fada kan mai uwa da wabi a makarantu da kuma wuraren da mutane suka taru.

Gwamnatin Trump ta ce zata inganta matakan tsaro a makarantu, to amma bata bukaci a zatar da wata sabuwar doka akan ikon mallakar bindiga ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG