Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa Sun Zura Ido Su Ga Jam'iyyar Da Zata Yi Rinjaye a Majalisar Dattawan Kasar


Har zuwa yau Laraba ba a tabbatar da jam’iyyar da za ta kasance mai rinjaye ba a majalisar dattawan Amurka a zabuka zagaye na biyu guda biyu da aka yi a jihar Georgia da ke kudancin kasar.

Bisa ga sakamakon da aka samu ya zuwa yanzu ‘yan Democrat na gab da samun rinjaye a majalisar yayin da Rev. Raphael Warnock na jam’iyyar Democrat ya yi hasashen samun galaba kan Sanata Kelly Loeffler a zaben wanda aka yi ranar Talata 5 ga watan Janairu.

Kafafen yada labaran Amurka sun nuna cewa Warnock da ke kan gaban Loeffler ne ya lashe zaben da kuri’u fiye da 40,000 yayin da aka kusan kammala kidayar kuri’un.

A dayan zaben, dan takarar jam’iyyar Democrat Jon Ossoff, mai hada wasu shirye-shiryen talabijin, shi ne ke kan gaban David Perdue na jam’iyyar Republican, wanda ke neman wani wa’adin, da sama da kuri’u 12,000.

A halin da ake ciki kuma, yau Laraba ‘yan majalisar dattawa da ‘yan majalisar wakilan Amurka zasu yi wani zama a majalisar dokokin kasar don kidaya da kuma tabbatar da kuri’un wakilan zabe bisa ga sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a watan Nuwamban da ya gabata.

Da ma wannan wani abu ne da aka saba yi, ya na zaman mataki na karshe bayan da wakilan zabe suka zabi Joe Biden a hukumace ranar 14 ga watan Disamban da ya gabata, abinda kuma ya zama wani abin gwaji ga ‘yan majalisar jam’iyyar Republican da ke goyon bayan shugaba Donald Trump. Masu goyon bayan Trump fiye da 100 ke shirin kalubalantar tabbatar da sakamakon zaben.

Bisa ga gyaran da aka yi a kundin tsarin mulkin Amurka na 12, dole ne dukkan majalisun su zauna don kidayar kuri’ da kuma tabbatar da sakamakon kuri’un wakilan zabe daga jihohi 50 na Amurka da gundumar Columbia a hukumace.

XS
SM
MD
LG