Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Na Kara Samun Goyon Bayan 'Yan Republican


Ana samun karin ‘yan majalisa daga jam’iyyar Republican da ke goyon bayan kokarin shugaba Donald Trump na sauya sakamakon zaben kasar da aka yi.

Sanatocin sun yi alkawarin zasu kalubalanci sakamakon idan majalisar dokokin kasar ta yi zamanta a mako mai zuwa don kirga kuri’un wakilan zabe da kuma tabbatar da nasarar da shugaba Joe Biden mai jiran gado ya samu.

A jiya Asabar ne Sanata Ted Cruz na jihar Texas ya sanar da cewa wasu sanatoci su 11 sun hada kai zasu marawa kokarin Trump baya na yin watsi da abinda Amurkawa suka zaba.

A halin da ake ciki kuma, wasu bata gari sun auna gidajen shugaban majalisar dokokin Amurka Mitch McConnell na Republican da shugabar majalisar wakilai Nancy Pelosi ta Democrat, inda suka yi wasu rubuce-rubuce, suka kuma ajiye jinin bogi da kan alade a gidan, a cewar kafafen yada labaran Amurka.

Bata garin sun yi rubuta a jikin kofa da tagar gidan MacConnell da ke Louisville a jihar Kentucky “ina kudinmu suke, da kuma "Mitch ya kashe talakawa." A cewar kafafen yada labaran Amurka.

Ita kuma Nancy Pelosi aka ajiye kan alade da jinin bogi a wajen gidanta da ke San Francisco a jiya Asabar, a cewar kafafen yada labaran yankin.

An auna gidajen manyan yan majalisar daga Republican da Democrat ne bayan zazzafar muhawara da ake yi akan tallafin coronavirus.

XS
SM
MD
LG