Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Aza tutar Sudan Ta Kudu A Majalisar Dinkin Duniya


Tutar Sudan ta kudu a tsakiya, a kofar Majalisar Dinkin Duniya,bayan an maince da shigarta Majalisar.

An aza tutar sabuwar ‘yantacciyar kasar Sudan ta kudu a harabar MDD, bayan ta zama kasa ta 193 na majalisar a jiya Alhamis.

An aza tutar sabuwar ‘yantacciyar kasar Sudan ta kudu a harabar MDD, bayan ta zama kasa ta 193 na majalisar a jiya Alhamis.

Daruruwan jami’an jakadanci ne suka hallara a helkwatar majalisar dinkin Dunkiya dake New York, domin bikin aza tutar, bayan da babban zauren ya amince d a shigar da Sudan ta kudu a kuri’ar da suka kada ta wajen daga hanu.

Haka ma ana ci gaba da na’am da kafuwar kasar, domin ko a yau jumma’a ma hukumar sadarwa ta MDD ta bada lamba 211 ta zame lambobin farko da mai kira a woya zai buga domin kiran ko wace lambar a Sudan ta kudu.Sudan ta kudun ce ta nemi haka.

Lambar shaida ce ta shekarar da Sudan ta kudun ta zama kasa mai ‘yancin kai, bayan da al’umar kasar suka amince da kuri’ar raba gardama da aka yi cikin watan janairu.

XS
SM
MD
LG